An rage dakatarwar da aka yiwa Samuel Eto'o

etoo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Samuel Eto'o

Kwamitin zartarwa na hukumar dake kula da kwallon kafa a Kamaru-Fecafoot ta rage yawan dakatarwar da aka yiwa Samuel Eto'o ya zamo dakatarwar watanni takwas.

A daren ranar Juma'a ne suka dauki matakin bayan wata tattaunawa mai tsawo.

Tsohon gwarzon dan kwallon Afrika din kenan ba zai buga wasanni hudu ba na Kamaru daga nan zuwa watan Agusta.

Wato wasannin farko farko na neman gurbin zuwa gasar kwallon kasashen Afrika na 2013 da kuma na kofin duniya a 2014.

Shugaban Kamaru Paul Biya shima ya bukaci jami'an Fecafoot su sake duba matakin da suka dauka.

An dakatar da Eto'o ne saboda jagorantar 'yan wasan Indomitable Lions suka yi yajin aiki akan batun alawus.

A lokacinne kuma 'yan wasan Kamarun suka ki buga wasan sada zumunci tsakaninsu da Algeria a watan Nuwamba.

Karin bayani