Tennis:Murray ya lashe gasar Brisbane Open

Andy Murray Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andy Murray

Andy Murray na shirye shiryensa na gasar Australian Open a cikin nasara bayan ta lashe gasar Brisbane Open sakamakon nasararsa akan Alexandr Dolgopolov a wasan karshe.

Murray ya nunawa Dolgopolov ruwa ba tsaran kwando bane inda ya doke shi da seti biyu a jere.

Murray yace "naji dadin wannan nasarar kuma ina saran wasu a nan gaba".

Shi kuwa Jo Wilfred Tsonga ya lashe gasar Qatar Open ne bayan ta doke dan uwanshi bafaranshe Geal Monfils a wasan karshe.

Wannan ne kofin na takwas a gasar ATP da Tsonga ya lashe.

Gasa ta gaba itace Australian Open wanda za a soma a ranar 16 ga watan Junairu a birnin Melbourne.