FA: Manchester United ta doke City daci 3 da 2

rooney Hakkin mallakar hoto e
Image caption Rooney da Wellback suna murnar doke Man City

Manchester United ta sha da kyar a hannun Manchester City daci uku da biyu a wasan zagaye na uku da suka buga na gasar cin kofin FA na Ingila.

Wasan da aka buga a filin Etihad, ya ja hankalin jama'a a yayinda alkalin wasa ya kori kyaftin din City Vincent Kompany mintuna goma sha biyu da fara wasan.

Har wa yau, Paul Scholes wanda yayi ritaya a bara, ya koma bugawa United saboda karancin 'yan wasan da take fama da shi sakamakon rauni.

Manchester United ta zira kwallayenta ne tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, inda Rooney yaci kwallaye biyu a mintuna na goma da kuma arba'in a yayinda Wellback yaci daya a minti na ashirin.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci sai Kolarov ya farkewa City kwallo daya sannan kuma Sergio Aguero ya zira ta biyu.

Itama Chelsea ta samu nasara a wasanta bayan ta lallasa Portsmouth daci hudu da nema.

Mata da Ramires da kuma Frank Lampard ne suka ciwa Chelsea kwallayenta.