Hughes na kan gaba wajen zama kocin QPR

hughes Hakkin mallakar hoto elvis
Image caption Mark Hughes

Mark Hughes shine kan gaba na zamowa kocin Queens Park Rangers, a yayinda shugaban kulob din Philip Beard zai sanarda sabon mai horadda 'yan wasan nan da sa'o'i arba'in da takwas.

Tsohon kocin Wales din mai shekaru 48, ya jagoranci Fulham kafin a sallameshi a watan Yuni, kuma tun lokacin baida kulob.

Beard ya shaidawa BBC cewar "muna aiko tukuru don daukar wanda ya dace".

Ina saran zamu samu wani kafin wasanmu da Newcastle.

Mark Hughes ya taba zama kocin Blackburn da Manchester City.

An sallami kocin QPR Neil Warnock ne saboda kulob dinne na goma sha bakwai a teburin gasar Premier.

Tsaffin masu horadda 'yan wasa a QPR:

* 2010-12: Neil Warnock * 2010: Mick Harford (Riko) * 2009-10: Paul Hart * 2009: Steve Gallen & Marc Bircham (Riko) * 2009: Jim Magilton * 2009: Gareth Ainsworth (Riko) * 2008-09: Paulo Sousa

Karin bayani