An nada Hughes a matsayin kocin QPR

hughes Hakkin mallakar hoto elvis
Image caption Mark Hughes

Mark Hughes ya kulla yarjejeniyar shejaru biyu da rabi a matsayin sabon kocin kungiyar Queens Park Rangers.

Dan kasar Wales din ya maye gurbin Neil Warnock a Loftus Road wanda aka kora a ranar Lahadi.

QPR ce ta goma sha bakwai akan teburin gasar Premier kuma ta buga wasanni takwas a jere ba tare da samun nasara ba.

Hughes mai shekaru 48 ya bar Fulham ne a watan Yuni sannan a baya ya jagoranci Wales, Blackburn Rovers da kuma Manchester City.

QPR ta dawo bugawa ne a gasar premier a kakar wasan data wuce a karkashin Warnock.