Inter ta soma tattaunawa da City akan Tevez

tevez Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Carlos Tevez

Manchester City ta soma tattaunawa da Inter Milan akan sayen Carlos Tevez.

City ta tattaunawa da AC Milan amma sai cinikin bai kaya ba saboda Milan din tafi son dan kwallon a matsayin aro ba wai batun dun-dun-dun ba.

Wakilin Tevez ya gana da mahukunta a Inter amma kuma babu yarjejeniya akan batun kudi.

Shi dai dan wasan na Argentina yafi son ya koma AC Milan a yayinda ake kokarin kamalla yarjejeniya kafin a rufe kasuwar musayar 'yan kwallo.

Shugaban Inter Milan Massimo Moratti ya ce "duk abinda ya kamata ayi me kyau, ya kamata a gaggauta yinsa".

Tevez bai bugawa City kwallo ba tun wasanta da Birmingham a ranar 21 ga watan Satumba.

An samu rashin jituwa ne tsakanin kocin City Roberto Mancini da Carlos Tevez inda kocin yayi zargin cewar Tevez ya ki yarda ya shigo fili ya buga kwallo bayan an dawo hutun rabin lokaci a wasan City da Bayern Munich.

Karin bayani