Dan Chelsea Kakuta ya koma Dijon na wucin gadi

kakuta Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gael Kakuta

Dan kwallon Chelsea Gael Kakuta ya koma kungiyar Dijon ta Faransa a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Kakuta mai shekaru 21 bai bugawa Chelsea ba a kakar wasa ta bana sannan ya tafi Bolton a matsayin aro.

A kakar wasan data wuce Chelsea ta bada Kakuta din zuwa Fulham inda ya zira kwallo daya a cikin wasanni bakwai.

Dijon ce ta bada bayanin kwangilarta da Kakuta a shafinta na intanet amma bata bada karin bayani ba.