Keane ya koma Aston Villa na wucin gadi

keane Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Robbie Keane

Aston Villa ta sayi dan wasan Los Angeles Galaxy da Jamhuriyar Ireland Robbie Keane a matsayin aro har zuwa ranar 25 ga watan Fabarairu.

Keane ya ce "kwangilar ta gajeren lokaci ne".

A baya ya bugawa Coventry da Leeds da Spurs da kuma Liverpool.

Keane mai shekaru 31 yayi horo tare da Villa kuma watakila ya buga wasansa na farko a ranar Asabar tsakaninsu da Everton.

Ya soma taka leda ne tare da Wolverhampton Wanderers a matsayin dan shekara 17 inda ya bayyana "na ji dadin komawa gasar premier ta Ingila".

Kocin Villa McLeish a bara ya nemi sayen Keane lokacin yana jagorancin kungiyar Birmingham City amma dan wasan ya koma Amurka.