Mancini ya yi cacar baki da Gerarrd

manicni Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Roberto Mancini

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya yi cacar baka tsakaninsa da kyaftin din Liverpool Steven Gerrard bayanda City ta sha kashi daci daya me ban haushi a wasan gasar kofin Carling.

Mancini ya ce harin da Glen Johnson ya kaiwa Joleon Lescott kamata yayi a ladabtardashi, a cewarsa harin yafi wanda aka baiwa Vincent Kompany jan kati.

Amma kuma Gerrard yaki amincewa da ra'ayin Mancini.

A lokacin Mancini na jiran 'yan jarida su tattauna sai Gerrard te matsa kusadashi don nuna kin yardarsa.

Kyaftin din Liverpool ya nunawa kocin City dan yatsa yana ce masa "Kace Wayne Rooney ne ya sanya aka kori Kompany, amma kaima kanason a kori Jonhson".