United ta doke Bolton daci uku da nema

rooey Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rooney da Wellback

Manchester United ta kamo City a yawan maki a gasar premier bayan ta lallasa Bolton daci uku da nema.

Paul Scholes da Danny Welback da kuma Micheal Carrick ne suka ciwa United kwallayenta abinda ya bata damar samun maki arbain da takwas daga wasanni ashirin da daya.

Sakamakon sauran karawar da aka yi a Ingila:

* Aston Villa 1-1 Everton * Blackburn 3-1 Fulham * Chelsea 1-0 Sunderland * Liverpool 0-0 Stoke * Tottenham 1-1 Wolves * West Brom 1-2 Norwich