Arsenal zata yi rangadi zuwa Najeriya

arsena; Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Arsenal zata kawo ziyara a karon farko a Afrika

Arsenal na shirye shiryen zuwa rangadi a Najeriya a karshen kakar wasa ta bana.

Jami'an kungiyar sun ziyarci Najeriya a watan daya gabata don duba filayen wasa sannan kuma suka tattauna da jami'an hukumar kwallon Najeriya wato NFF akan batun rangadin da ake shirin yi a watan Yuli.

A ranar Juma'a wadanda suka shirya rangadin wato DanJan Sports suka tattauna da jami'an Arsenal a filin Emirates don kamalla shirye shiryen.

Darektan kasuwanci na Arsenal Angus Kinnear ya shaidawa BBC cewar "Komai na tafiya yadda ya kamata. Ziyara zuwa Najeriya zai yiwu".

Ya kara da cewar "akwai mahimmaci matuka mu aika sako ga magoya bayanmu a yammacin Afrika da nahiyar baki daya".

A bisa tsarin dai, Arsenal na gudanar da horon kamalla kakar wasa ne a filinta na Emirates, amma saboda gasar Olympics wannan karon shine yasa zata zo nahiyar Afrika a karon farko a tarihinta.

A watan Yulin 2008 ne kamfanin DanJan Sports ya kawo Manchester United da Portsmouth, suka fafata a wasan sada zumunci da Kano Pillars.