An fara atisayen tsaron Olympics a kogin Thames

Jiragen ruwa a cikin Thames Hakkin mallakar hoto BBC screen grab
Image caption Jiragen ruwa a cikin Thames

Hukumar 'yan sandan birnin Landan da sojojin ruwa sun fara wani atisaye na tsaro a kan kogin Thames kafin a fara gasar Olympics a watan Yuli mai zuwa.

Kimanin 'yan sanda 44, da sojoji 94 da jiragen ruwan yaki 15 da helikwaftoci ne za su ci gaba da atisayen har zuwa ranar Juma'a mai zuwa.

Mataimakin kwamishinan 'yan sandan birnin Landan Chris Allison ya ce atisayen, ba shi da nasaba da wata barazana.

Matakan tsaron gasar ta Olympics da za a shafe kwanaki 64 ana gudanar wa, za su lashe kimanin fam miliyan 600.

Wata sanarwa da ta fito daga hukumar 'yan sandan birnin Landan ta ce, atisayen na kogin Thames an shirya shi ne, domin dukkan jami'an tsaro su san yadda kogin ke gudana da kuma dabarun da za a yi amfani da su.

Karin 'yan Sanda

Za a fara fuskantar kalubalen tsaro ne gadan-gadan a lokacin da za a bude kauyen Olympics a ranar 13 ga watan Yuli.

Hakan kuma zai ci gaba har sai an rufe kauyen a ranar 12 ga watan Satumba.

Jami'an tsaro za su kula da jimillar cibiyoyin wasan Olympics 34 a duk fadin Burtaniya.

Hukumomin 'yan sanda 11 da kuma jami'an soji ne za su shiga aikin samar da tsaron.