Cahill ya kamalla yarjejeniyarsa a Chelsea

cahill
Image caption Gary Cahill

Chelsea ta kamalla kulla yarjejeniyar sayen dan kwallon bayan Bolton Gary Cahill akan kusan fan miliyon bakwai.

Cahill mai shekaru 26 a ranar Asabar aka gwada lafiyarsa a Chelsea kafin yaje ya kalli wasan da Blues din suka doke Sunderland daci daya me ban haushi a filin Stamford Bridge.

Cahill yace "Chelsea babban kulob ne dake da niyar lashe kofuna da dama".

Ya kara da cewar "babbar dama ce na samu don in bada gudumuwa ta".

Cahill ya soma taka leda ne a Aston Villa kafin ya tafi aro a kulob din Burnley daga nan ya koma Bolton akan fan miliyon biyar a shekara ta 2008.

Ya kasance dan Ingila na biyar a kulob din kuma zai rike bayan Chelsea tare da John Terry.

Sauran 'yan Ingilan dake Chelsea kuwa sune Frank Lampard, Ashley Cole da kuma Daniel Sturridge.