Ghana ta yi murna akan Essien

essien Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Micheal Essien

Hukumar kwallon Ghana-GFA ta bayanna jindadinta akan komawar dan kwallon Chelsea Micheal Essien bayan jinyar raunin da yayi.

Dan kwallon ya shafe watanni shida yana jinya sannan kuma za a kara buga gasar cin kofin kasashen Afrika da za ayi a Gabon da Equatorial Guinea.

Shugaban GFA Kwesi Nyantakyi a wata sanarwa ya ce murmurwar Essien babban cigaba ne ga kasar da kuma kulob dinsa.

Sanarwar ta ce "Hukumar kwallon Ghana tayi murnar ganin Micheal Essien ya koma horo a kokarinsa na komawa taka leda".

Shugaban ya kara da cewar zasu baiwa dan wasan duk gudun muwar da yake bukata.