Inter Milan ta taya Tevez akan fan miliyon 20.7

tevez Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Carlos Tevez

Inter Milan ta bada tayin fan miliyon 20 da digo bakwai akan Carlos Tevez, amma kuma bai kai abinda Manchester City ta saka akan dan Argentina din ba.

Shugaban Inter Massimo Moratti ya ce "mun bada tayin Euro miliyon ashirin da biyar, yanzu ya rage nasu su yarda ko kuma kada su yarda".

Ya kara da cewar "mun bada tayin, a yanzu hukunci ya rage nasu".

AC Milan ta janye batun sayen Tevez mai shekaru 27 ne bayanda Alexandre Pato ya ce ya fasa komawa Paris St Germain.

Milan ta riga ta sasanta tsakaninta da dan kwallon kafin kulob din ya janye daga tattaunawar.

PSG itama ta nuna sha'awarta akan Tevez a yayinda Moratti yace akwai wasu kulob a Ingila dake zawarcin dan wasan.

Tun a ranar 21 ga watan Satumba rabon da Tevez ya bugawa Manchester City kwallo.