Clinton ya jinjinawa Muhammed Ali

mohammed ali Hakkin mallakar hoto THOMAS HOEPKER
Image caption Muhammed Ali

Tsohon shugaban Amurka Bill Clinton ya jinjinawa shahararren dan wasan dambe Muhammed Ali saboda kwarjininsa da akidojinsa da suka janyo yayi fice a duniya.

Clinton wanda ya bayyana haka a cikar Ali shekaru saba'in a duniya, ya kara da cewar dan damben ya taka muhimiyar rawa wajen ganin Barack Obama ya zama shugaban Amurka bakar fata na farko.

Clinton yace "Ya sa miliyoyin mutane sun gane cewar yanada baiwa ta musamman".

Zakaran damben duniya har sau uku, ya samu nasara a karawa 56 a cikin shekaru ashirin da daya.

Muhammed Ali ya kara suna a duniya bayan da yaki amincewa ya shiga cikin yakin da Amurka keyi a kasar Vietnam.