Rauni zai hana dan Mali Traore taka leda

Kalilou Traore
Image caption Kalilou Traore

Dan kwallon Mali Kalilou Traore ba zai buga gasar cin kofin Afrika ba sakamakon kasa murmurewa daga rauni a gwiwarsa.

Wannan dai ya zowa kocin kasar Alain Giresse da bazata saboda ya zaci dan wasan zai warke kafin gasar ta kwallon Afrika.

Kocin yace"Abu ne mara dadi mun kara rasa wani dan wasan".

Traore mai shekaru 24 ya riga ya fice daga sansanin 'yan wasan Mali dake Togo.

Wani labarin kuma shima Mohammed Fofana yana fama da rauni abinda ke nuna rashin tabbas akan ko za a buga gasar tare dashi.

Haka zalika, rahotanni daga Malin na nuna cewar dan wasan Auxerre Adama Coulibaly shima ba zai bugawa Mali din ba saboda karayarsa bata warke ba.