Beckham ya sabunta kwangilarsa a Galaxy

beckham Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption David Beckham

David Beckham zai cigaba da taka leda a LA Galaxy bayan sanya hannu a sabuwar kwangila ta karin shekaru biyu a kulob din.

Tsohon kyaftin din Ingila mai shekaru talatin da shida, kungiyar PSG ta Faransa ta nemeshi amma sai ya yanke shawarar cigaba da kasancewa da kulob din na Amurka.

Beckham yace "Wannan shawara ce me kyau gare ni".

Ya kara da cewar "kungiyoyi da dama sun nuna sha'awa akai na, amma inda burin cigaba da bugawa a Amurka".

Daga Manchester United, Beckham ya koma Real Madrid a shekara ta 2003 akan fan miliyon ashirin da biyar kafin ya koma Amurka a kwangilar data kai fan miliyon 128 na tsawon shekaru biyar.

Karin bayani