Nadal da Federer sun kai zagayen kwata final

Nadal da Federer Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Nadal da Federer

A gasar Australia Open na Tennis. Rafael Nadal da Roger Federer sun tsallake zuwa wasan kwata final.

Shi dai Nadal bai fuskanci wata matsala ba wurin doke dan kasar sa Feliciano Lopez kai tsaye ba tare da wata matsala ba.

A halin yanzu dai Nadal zai kara ne tare da Tomas Berdych wanda shi kuma ya doke Nicolas Almagro.

Shi kuwa Roger Federer ya karya alkadarin dan kasar Australia ne wato Bernard Tomic wanda yan kasar ke burin ganin ya yi tasiri a gasar.

A yanzu dai, Federer zai kara ne da Juan Martin del Potro wanda ya doke shi a wasan US Open a shekarar 2009.