Manchester City ta sha da kyar a hannun Tottenham

Manchester City Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Manchester City

Manchester City ta yi nasara kan Tottenham da kyar da ci ukku da biyu, bayan da Mario Balotelli ya zura kwallo a bugun daga kai sai gola ana sauran yan mintoci kadan a tashi wasa.

Jermain Defoe kiris ya rage ya jefawa Tottenham kwallo a ragar Manchester City, to amma ya kuskure.

Wannan ce nasara ta goma sha daya a jere da Manchester City ta samu a gida cikin wannan kakar wasan na bana.

City dai ta sha kwallaye biyu ne cikin mintuna 4 kacal, amma Tottenham ba ta yi wata wata ba ta farke.

A yanzu dai City ta kara hawa da maki 8 gaban Tottenham inda Manchester United ce kadai tsakanin su.