Ivory Coast ta sha da kyar a wajen Sudan

drogba Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Didier Drogba

Ivory Coast ta fara gasar cin kofin kasashen Afirka da kafar dama bayan data doke Sudan da kyar daci daya daya da nema.

Kyaftin Didier Drogba ne dai ya fara kai farmaki bayan da yayi kokarin jefa kwallon da Solomon Kalou ya shura masa ,to amma hakar su bata cimma ruwa ba duk da ana ganin zasu tabuka abin azo a gani kafin fara wasan.

A bisa dukkan alamu dai Sudan ta kamala wasan tana farin ciki ganin yadda ta hana Ivory Coast sakat duk da tana kunshe da 'yan wasa da dama dake taka leda a Turai.

Tun daga farkon wasan dai, a kwai alamun Sudan ta shiga filin wasa ne da aniyar dagulawa Ivory Coast lissafi, inda Sudan wacce ke ta 120 a jerin kasashe na FIFA, hankali kwance sun rinka tsayawa a baya, inda don mayar da 'yan Ivory Coast din baya yayin da suka yunkura don kai hari.

A 'yan lokuta kalilan da Ivory Coast ta yunkura har ta dangana da yankin 18 na Sudan, bata iya zira kwallo a ragar Sudan ba, haka kuma Gervinho ya barar da wata babbar dama daya samu.

Ya dauki Ivory Coast wani dogon lokaci kafin Idanuwan su su bude, to amma duk da sun yi ta kokarin kai bara,basu iya gigita yan Sudan ba.

Daga bisani ne dai Didier Drogba ya yunkuro ,ya kuma cafe wata kwallo da Kalou ya mika masa inda kamar guguwa ya baiwa mai tsaron gidan Sudan Elmuez Maghoub mamaki, ya kuma sami kwallo ta 51 a wasanni kasa da kasa.

'Yan Sudan sun shiga fili bayan hutu rabin lokaci da kuzarin kai bara, hakar su kuma ta kusa cimma ruwa bayan da Eltaib Mudather ya kai hari to amma sai mai tsaron gidan Ivory Coast Boubacar Barry ya tura kwallon waje.

Mudather yayi ta kai bara yayin da wasan ya ci gaba to amma bai sami nasara ba,yayin da suma a bangaren Ivory Coast Gervinho da Drogba suka barar da kwallaye.

Yan Ivory Coast zasu kasance cikin farin ciki bayan samun nasara a wasan suna farko na rukunni B, to amma a gaskiya sai sun sake zage Dantse idan suna son tabbatar da kallon da ake musu kafin fara Gasar.