Kamata yayi a kori Balotelli-Redknapp

redknapp Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Harry Redknapp

Manajan Tottenham Harry Rednapp na ganin kamata yayi ace an kori Mario Balotelli saboda laifin haurin Scott Parker a ka a wasan su da Manchester City inda aka tashi Tottenham nada kwallaye 2 City nada 3.

Alkalin wasa Howard Webb dai bai hukunta Mario Balotelli ba bayan daya hauri Scott Parker da ganganr laifin kuma ya faru ne bayan da dama an baiwa Balotelli katin gargadi.

Harry Rednapp ya bayyana cewa yana ganin ya kamata ace an baiwa Balotelli jan Kati.

Balotelli wanda ya shiga wasan bayan hutun rabin lokaci, ya shiga wata yar sarkakiya da Parker, inda al'amari na fari yayi kama da tsautsayi,to amma na biyu yayi kama da kai hauri da gangan da kafa zuwa Parker.

Manajan na Tottenham yace daga farko kamar bada gangar ya kai hauri ba,to amma hauri na biyu kai tsaye da gangar ya kaiwa Parker duka a ka.

Manajan Tottenham ya kara fusata ne bayan da Balotelli ya zira kwallo a ragar Tottenham a wani bugun daga kai-sai -mai tsaron gida,kwallon data tabbatarwa da Manchester City matsayin ta a saman rukunin klub klub na gasar Premier bayan da Ledley King ya haure shi.

Wannan nasara da City ta samu a bisa Tottenham dai ta mayar dasu baya da maki 8 tsakanin su da wadanda ke gaba wato Manchester City.