Australian Open: Federer da Nadal za su fafata

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rafeal Nadal da Roger Federer, abokan hammaya ne a wasan Tennis

Roger Federer zai fafata da Rafael Nadal a wasan kusa dana karshe a gasar Australian Open.

Federer ya doke Juan Martin Potro a wasan dab da kusa dana karshe a wasanni uku a jere a yayinda shi ku ma Nadal ya doke Tomas Berdych.

Bayan wasan da Nadal din ya doke Berdych ya nuna cewa ya gaji sosai saboda wasan ya bashi wahala.

"Gaskiya na sha wahala a wasa na biyu, amma a na uku da hudu na jajirce. Ina farin ciki saboda na gama da kwari na." In ji Nadal.

Federer dai ya kafa tarihi a gasar ta bana saboda ba a doke shi a wasa ko guda ba ya zuwa yanzu.