QPR da Chelsea za su dauki mataki

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ana tuhumar Terry da yiwa Ferdinand kalamun wariyar launin fata

Kungiyar QPR da Chelsea sun ce za su dauki mataki a kan magoya bayansu da za su yi kalamun batanci a wasan da kungiyoyin biyu za su buga a gasar cin kofin FA a ranar asabar.

Wasan shine na farko tun bayan cece kucen da aka samu a lokacin da su ka hadu a watan Okutoban bara.

An dai zargi Terry ne da yin kalamun wariyar launin fata ga Anton Ferdinand.

A wata sanarwa da Kungiyoyin biyu su ka fitar, sun ce ba za su amince da nuna banbanci a harkar kwallon kafa ba.

A ranar Talata ma Kungiyar QPR ta bukaci Ferdinand da ya gaisa da Terry kafin a fara wasan.

Masu shigar da kara a Ingila dai na tuhumar Terry da yi wa Ferdinand kalamun wariyar launin fata.