Ghana ta sha da kyar- Asamoah Gyan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Asamoah Gyan

Dan wasan Ghana Asamoah Gyan ya nace cewa kasarsa na cikin sahun kasashen da za su iya lashe gasar cin kofin Afrika duk da cewa dai da kyar ta sha a hannun Botswana.

Ghana dai ta doke Botswana da kwallo daya tilo ne, kuma kungiyar ta sha da kyar ne.

Amma dan wasan gaban Ghana din ya shaidawa BBC cewa kasar za ta zage damtse nan gaba a yayinda aka ci gaba da gasar.

Ya ce Ghana ta samu sa'a ne a wasan da ta doke Botswana.

"Gaskiya mun yi sa'a da mu ka yi nasara, amma 'yan wasan sun nuna kwarewa," In ji Gyan.

"Wasan farko yana da wahala sosai a koda yaushe amma abun mahimmaci a nan shine muna da maki uku."