Van Persie ya musanta rashin jituwa da Wenger

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kyaftin din Arsenal, Robin Van Persie

Dan wasan Arsenal Robin van Persie ya musanta cewa akwai rashin jituwa tsakaninsa da kocin kungiyar duk da cewa dai ya nuna rashin jin dadinsa a lokacin da kocin ya sauya Alex Oxlade-Chamberlain a wasan da kungiyar ta buga a ranar Lahadi.

An dai sauya matashin dan wasan ne ana saura minti 16 a tashi wasan da kungiyar ta buga da United, abun da kuma yasa magoya bayan kungiyar suka rikawa kocin ihu.

Van Persie ma ya nuna rashin gamsuwa da sauyin da kocin ya yi amma ya ce babu rashin jituwa tsakaninsu.

"Babu wata matsala, babu rashin jituwa, ba cece kuce." In ji Van Persie.

"Ba wai ina kalubalantar matakin da kocin ya dauka bane. Nasan bani da hurumin in kalubalanci abun da Wenger ya yi.

"Ba wai na nuna fushi na ga kocin bane a ranar Lahadi, na dai nuna rashin jindadi ne a lokacin da aka sauya Alex saboda shiya bani kwallon da na zura.

"Alex na fama da rauni amma bamu sani ba. Ina ganin abun da yasa kocin kenan ya sanya Andrey Arshavin."

"Wenger dai bai ambaci cewa dan wasan na da rauni ba a hirar da ya yi da manema labarai bayan wasan, ya dai ce ne dan wasan ya samu rauni ne saboda ya gaji.