Equatorial Guinea ta tsallake zuwa Q/Final

Daya daga cikin kasashen dake daukar nauyin bakuncin gasar cin kofin Afrika wato Equatorial Guinea ta tsallake zuwa zagayen wasan gab da kusa dana karshe.

Kasar dai ta bada mamaki ne bayan da ta doke Senegal da ci biyu da daya a wasanta na biyu.

A wasan farko da kungiyar ta buga ta doke Libya ne da ci daya mai ban haushi.

A yanzu haka dai an fidda Senegal a gasar, amma tana da sauran wasa daya.

"Gaskiya mun yi sa'a sosai muka zura kwallo dab da an kusan a tashi wasan. Muna da kwarin gwiwa zamu doke Zambia domin mu jagoranci rukunin da muke." In ji Juvenal Edjogo, kyaftin din Equatorial Guinea.

A daya wasan da aka buga a rukunin na A, Libya ce ta tashi biyu da biyu tsakaninta da Zambia.