Austrailian Open: Nadal ya doke Federer

Hakkin mallakar hoto AP

Rafael Nadal ya nuna kwarewarsa inda ya doke Roger Federer a wasan kuda da na karshe a gasar Tennis ta Austrailian Open.

A yanzu haka dai Rafeal ya tsallake zuwa wasan karshe wanda za'a buga a ranar Lahadi.

Dan wasan zai fafata da wanda ya yi nasara ne tsakanin Novak Djokovic da Andy Murray.

Nadal wanda a yanzu haka shine na biyu a fagen Tennis ya lashe gasar ta Austrailian Open da aka shirya a shekara ta 2009.