QPR ta sayi Nedum Onuoha daga City

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nedum Onuoha asalin dan Najeriya ne

Kungiyar Queens Park Rangers ta kammala siyan dan wasan Manchester City Nedum Onuoha na tsawon shekaru hudu da rabi.

Dan wasan ya taka leda karkashin Mark Hughes a lokacin da yake horon kungiyar Manchester City.

Ya zuwa yanzu dai ba'a bayyana kudin da aka sayi dan wasan ba.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 25, ya taka leda ne a kungiyar Suderland a kakar wasan bara na wucin gadi, saboda baya samu damar taka leda a City.

"Na san Nedum sosai, kuma dan wasa ne da zai taimakawa kungiyar sosai." In ji Mark Hughes.

"A lokacin da yake taka leda a karkashi na a kungiyar Manchester City ya taka rawar gani sosai.

"Kwareran dan wasan baya ne, kuma zamu iya amfani da shi ko ta wani bangare."