Arsenal ta yi ba zata a gasar cin kofin FA

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kyaftin din Arsenal Robin van Persie

Robin van Persie ya zura fenarity biyu a yayinda Arsenal ta dawo daga baya ta doke Aston Villa a gasar cin FA.

Villa dai ta zura kwallaye biyu a ragar Arsenal kafin a tafi hutun rabin lokaci, inda Richard Dunne da kuma Darren Bent su ka ci mata kwallayen.

Amma da aka dawo hutun rabin lokaci sai Arsenal ta zura kwallaye uku cikin mintuna bakwai.

Theo Walcot ne ya zura kwallon daya fanshewa Arsenal aka zama biyu da biyu kafin Van Persie ya zura kwallo a fenarity da ya ba Arsenal nasara a wasan.

A yanzu haka dai Arsenal ta tsallake zuwa zagaye na biyar a gasar ta cin kofin FA.