AFCON: Ghana ta doke Mali

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan wasan Ghana su na murnar zura kwallo

Ghana na kan hanyarta na tsallakewa zuwa wasan dab da kusa da na karshe a gasar cin kofin Afrika, bayan ta doke Mali da ci biyu da nema.

Asamoah Gyan ne ya fara zura kwallon farko a bugun falan daya bayan da aka dawo hutun rabin lokaci.

Andre 'Dede' Ayew kuma ya zura ta biyu inda ya tsame 'yan wasan bayan Mali kafin ya zura kwallon.

Mali dai su gamu da rashin sa'a domin dan wasanta Cheick Diabate ya yi kararrawa har sau biyu a sandan ragar Ghana.

Kasashen biyu sunyi taka tsan-tsan sosai a wasan kafin a tafi hutun rabin lokaci, saboda kowannen su na da kwarewa.