McLeish ya nemi dau mataki a kan Van Persie

Hakkin mallakar hoto allsp
Image caption Kocin Villa, Alex Mcleish

Kocin Aston Villa, Alex McLeish ya yi kira ga Hukumar FA ta Ingila da ta bincike gulan da dan wasan Arsenal Robin van Persie ya yi a wasan da kungiyar ta fidda Villa a gasar cin kofin FA.

McLeish dai na ganin kyaftin din Arsenal din ya yiwa dan wasan bayansa Carlos Cuellar a wasan.

"Ya nuna karara cewa ya yi masa gula ne, ina kuma son FA su duba domin daukar mataki a kai." In ji McLeish.

Van Persie dai ya zura bugun fenarity biyu a wasan da Arsenal ta doke Villa da ci uku sda biyu, bayan Villa ce ta faa zura kwallaye biyu a ragar Arsenal kafin a tafi hutun rabin lokaci.

"Alkalin wasa bai dauki mataki a kan batun ba, ni kuma ban ce mishi uffan ba." In ji McLeish.