Bobby Zamora ya koma QPR

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bobby Zamora

Kungiyar Queens Park Rangers ta sayi dan wasan Fulham Bobby Zamora akan fam miliyan hudu.

Dan wasan dai ya koma Fulham ne akan fam miliyan hudu da dubu dari takwas daga West Ham a watan Yunlin shekara ta 2008.

A farko wannan watan dai kocin Fulham, Martin Jol ya yi watsi da rahotannin da ke nuni da cewa dan wasan zai bar kungiyar saboda rashin jituwa tsakaninsu.

Zamora, ya zura kwallaye tara a wasannin 29 da ya buga a kasar wasan bana.