Wes Brown zai yi jinya na makwanni takwas

Hakkin mallakar hoto pa
Image caption Wes Brown ya takawa United leda kafin ya koma Sunderland

Dan wasan Sunderland Wes Brown zai yi jinya na makwanni takwas saboda raunin da ya samu a gwiwarsa.

Tsohon dan wasan Manchester United din ya samu rauni ne a gwiwarsa ne a wasan da kungiyarsa ta buga da Middlesbrough a gasar cin kofin FA, inda su ka tashi daya da daya.

Kocin Sunderland Martin O'Neill ya ce: "Muna ganin ba za'a yi mishi tiyata ba, amma zai kai kusan makwanni takwas yana jinya.

"Da farko ma, mun dauka ba zai buga wasa kuma ba a kakkar wasan bana."

Shima dai dan wasan tsakiyar kungiyar David Vaughan saboda ya jimu a idon sahunsa.