An sallami jami'an hukumar kwallon Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A kalla mutane 74 ne su ka rasa rayukansu a tarzomar da akayi a filin wasan

Firaministan Masar, Kamal Ganzouri ya bada sanarwar korar mambobin hukumar kwallon kafar kasar saboda rasa rayukan da aka yi a filin wasan kwallon kafa.

Ya kuma ce za'a binciki korarrun jami'an.

A kalla mutane 70 ne suka mutu a wani tashin hankali a filin wasan kwallon kafa a garin Port Said a ranar Laraba, bayan wasan da aka yi tsakanin Al-Ahly da Al masri.

Gwmanan garin ya ajjiye mukamin sa, kuma anyi tsit na minti daya a wani zaman gaggawa a majalisar dokokin kasar, a matsayin nuna alhini ga wadanda suka rasu.

Magoya bayan Al-ahly sun killace dandalin Tahrir a birnin Alqahira, saboda abunda suka kira gazawar 'yan sanda wajen hana aukuwar tashin hankalin.