Mancini ya dauki laifi game da kashin da City ta sha

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kocin Manchester City, Roberto Mancini

Kocin Manchester City, Roberto Mancini ya ce ya dau laifi game da rashin nasarar da kungiyar ta samu a wasan da ta buga da Everton.

Everton dai ta doke Manchester City ne da ci daya mai ban haushi.

Roberto Mancini dai ya ce bai shirya 'yan wasansa yadda ya kamata bane.

Duk da kashin da kungiyar ta sha, har yanzu ita ce ke ci gaba da jagoranci a gasar ta Premier.

"Gaskiya ina ganin laifi na ne, saboda bamu shiryawa wasan yadda ya kamata ba." In ji Mancini.

"Na dauka kafin wasan cewa ba zamu fuskanci matsala ba."