John Terry ba zai ajiye mukamin kyaftin ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption John Terry tare da Anton Ferdinand

Wata majiya mai karfi ta shaidawa BBC cewa dan wasan Ingila John Terry ba zai ajiye mukaminshi na kyaftin ba saboda ya fuskacin shari'ar zargin wariyar launin fata.

Dan wasan bayan Chelsea din zai fuskanci shari'a ne a ranar tara ga watan Yulin, saboda ana zarginsa da yiwa dan wasan QPR Anton Ferdinand kalamun wariyar launin fata a wasan da kungiyoyin biyu su ka buga a watan Okutoban bara.

"Ba zai sauka ba. Yayi imanin cewa bai yi laifi ba, kuma saboda haka ba zai ajiye mukamin ba." In ji Majiyar.

Dan wasan Reading, Jason Roberts ko cewa ya yi kada Terry ya taka leda a gasar cin kofin Turai.

Roberts, ya ce, halartar Terri gasar sai sanya rashin jituwa tsakanin 'yan wasan Ingila.

Za'a dai fara gasar na a ranar 8 ga watan Yuni a yayinda za'a kammala a ranar tara 1 ga watan Yuli, wasu 'yan kwanaki kafin a fara shari'ar John Terry.