Triesman ya yaba da mataki a kan Terry

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Tsohon shugaban hukumar FA na Ingila, Lord Triesman

Tsohon shugaban hukumar kwallon Ingila, Lord Triesman ya ya yi imanin cewa matakin da Hukumar FA ta dauka a kan John Terry na tsige shi daga mukamin kyaftin din Ingil ya yi dai-dai.

Kyaftin din Chelsea, Terry na jiran shari'a game da zargin kalamun wariyar launin fata da ya yiwa dan wasan QPR, Anton Ferdinand.

"Matakin ya yi daidai, ina farin cikin ganin David Bernstein ya dauki matakin da ya kamata." In ji Triesman.

"Abun da kawai ban amince da shi ba, shine yadda aka dauki tsawon lokacin kafin a dauki matakin."

An dai cire Terry daga mukamin kyaftin ne a ranar 3 ga watan Fabrairu ne sa'o'i 48 bayan da kotu ta ce za ta fara shari'a a kan sa a ranar 9 ga watan Yuli.

Tries ya ce babban zargi ne a kan Terry, sai kuma a wanke shi zai iya ci gaba da zama kyaftin din kasar.