Ghana da Mali sun kai wasan kusa da na karshe

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan Ghana na murnar zura kwallo

Ghana ta kai wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afrika bayan da ta doke Tunisia da ci biyu da daya a karin lokaci.

Kyaftin din Black Stars, John Mensah ne ya sa kungiyarsa a gaba minti tara da fara wasan, a yayinda Sabeur Khalifa ya fanshewa Tunisa kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Mai tsaron gida Carthage Eagles Aymen Mahtlouthi ya zubar da kwallo a karin lokaci, abun da kuma ya baiwa Andre 'Dede' Ayew damar zura kwallon da ya baiwa Ghana nasara.

A yanzu haka dai Ghana za ta buga wasan kusa dana karshe da Zambia.

Ita ko Mali ta cire daya daga cikin masu daukar nauyi gasar ne, wato Gabon a bugun fenarity.

Mali da ta lashe wasan ne da kwallaye biyar da hudu.

A cikin lokaci, kasashen biyu sun tashi daya da daya ne.