'Dakatar da Saurez da aka yi bai da ce ba'

Image caption Kocin Liverpool, Kenny Dalglish

Kocin Liverpool Kenny Dalglish ya yi maraba da dawowar Luis Suarez taka leda, kuma ya ce dakatarwar da aka yi mishi bai dace ba.

Suarez ya taka leda a wasan da Liverpool ta buga da Tottenham inda su ka tashi canjaras wato babu ci.

Hukumar FA ta Ingila ne dai ta dakatar da Luis Saurez na tsawon wasanni takwas bayan ta same shi da laifin yin kalamun wariyar launin fata a kan dan wasan Manchester United Patrice Evra.

"Ina matukar farin ciki da ya dawo taka leda, daman bai kamata a dakatar da shi tun farko ba." In ji Dalglish.

An dai sanya Suarez, a wasan da Liverpool ta buga da Tottenham ana minti 66 da wasan.