Kofin Afirka: Ivory Coast za ta kara da Zambia

'Yan wasan Zambia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan wasan Zambia suna murna bayan sun ci Senegal

Wasan karshe a Gasar cin Kofin Kwallon Kafa na Afirka zai kasance ne tsakanin Ivory Coast, wadanda aka fi baiwa fifiko, da kuma Zambia, wadanda ake yiwa kallon raini a gasar.

Wannan ne dai karo na uku da Zambia za ta buga wasan karshe a gasar—su ne suka zo a matsayi na biyu a shekarun 1974 da 1994.

Kafin su kai wannan matsayi na wasan karshe dai, a wasannin zagaye na farko, Zambia sun lallasa Senegal da ci biyu da daya; suka yi canjaras biyu da biyu da Libya, sannan suka yiwa Equatorial Guinea ci daya mai ban haushi.

A wasan daf da na kusa da na karshe kuwa, Zambia sun lallasa Sudan ne da ci uku da nema; yayin da a wasan kusa da na karshe suka yiwa Ghana ci daya mai ban haushi.

Gasar da suka halarta ta karshe ita ce wacce aka yi shekara guda bayan 'yan wasan Chipolopolo goma sha takwas sun rasa rayukansu a wani hadarin jirgin sama 'yan mintuna kadan bayan tashinsu daga babban birnin kasar Gabon, Libreville.

Komawarsu Gabon bayan wasanninsu biyar a Equatorial Guinea ya kara kwarin gwiwa ga 'yan wasan, wadanda shugaban Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Zambia Kalusha Bwalya ke yiwa jagoranci.

Shi dai Kalusha Bwalya ya tsallake hadarin jirgin na 1993 ne saboda a lokacin yana buga wasa a Turai.

"Karsashin da muke da ji ya sa ba ma jin tsoron kowa; ko da ya ke muna ganin kimar 'yan wasan Ivory Coast", in ji kocin Zambia, Herve Renard.

Ya kuma kara da cewa, "mun san ingancin 'yan wasan da abin da za su iya yi; ga mu nan ne dai a gaban tsauni, sai dai kuma karsashin da muke ji ya sa ba ma tsoron kaiwa kololuwa".

Su ma Ivory Coast wannan ne karo na uku da suke buga wasan karshe. A shekarar 2006 sun sha kashi a hannun Masar bayan sun yi nasara a kan Ghana a 1992, lokacin da suka yi nasararsu daya tilo.

Kafin su iso wasan karshe a wannan gasa kuwa, a zagaye na farko Ivory Coast sun yiwa Sudan ci daya mai ban haushi, sannan kuma suka lallasa Burkina Faso da ma Angola da ci biyu da nema.

A wasan daf da na kusa da na karshe kuma sun yi waje da Equatorial Guinea da ci uku ba ko daya, sannan suka yiwa Mali ci daya mai ban haushi a wasan kusa da na karshe.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin Ivory Coast, Francois Zahoui

'Yan wasan kungiyar Elephantsdin dai na fatan kasancewa na uku a tarihi da suka lashe kofin ba tare da an ci su ko da kwallo guda ba—su ne kuwa na farko da suka kafa wannan tarihi a shekarar 1992; sannan Kamaru suka kwata a shekarar 2002.

Bangaren Ivory Coast din dai cike yake da jaruman 'yan wasa irin su Didier Drogba, da Yaya Toure, da Gervinho, da kuma Didier Zokora.

Kocinsu, Francois Zahoui, wanda shi ne kocin gida na farko tun bayan Yeo Martial a shekarar 1992, da ya jagoranci kungiyar ta Elephants, ya ce babban aikinsa shi ne tabbatar da cewa 'yan tsaron bayansa sun yi aiki don kuwa ya san cewa da'iman 'yan wasansa na gaba za su ci kwallo.

Daya daga cikin wadannan 'yan wasa na gaba, Salomon Kalou, ya ce su ne za su daga kofin na Afirka don farantawa 'yan kasar Ivory Coast rai bayan tashin hankalin siyasar da suka gani a 'yan shekarun nan.

"Kasarmu ta sha fama da tashin hankali, saboda haka muna so mu yi nasara don farantawa mutanenmu wadanda suka jima suna shan wahala", in ji shi.

Ya kuma kara da cewa, "a matsayinmu na 'yan wasan kwallon kafa, abin kawai da za mu iya yiwa kasarmu shi ne mu zage dantse mu yi abin da mutanenmu za su yi alfahari da shi".

Karin bayani