Real Madrid ce kungiyar da ta fi kudi a duniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan kungiyar, Real Madrid

Kudaden shigar kungiyar Real Madrid ya kai euro miliyan dari hudu da tamanin a yayinda kungiyar ta ci gaba da zama na wadda ta fi kudi a duniya, in ji kamfanin Deloitte mai hada hadar harkar wasanni.

Bayanan da kamfanin Deloitte ya fitar ya maida hankali ne a kan kakar wasanni shekara ta 2010/2011.

Real Madrid dai ce ta daya na tsawon shekaru bakwai kenan a kiddigar da kamfanin ya fitar.

Abokiyar hammayar Real, wato Barcelona ce ta biyu a yayinda kuma Manchester United ta zama ta uku.

Bayern Munich ce ta hudu sannan Arsenal tana ta biyar, Chelsea dai ce ta shida a teburin.

Kungiyoyin kwallon kafa da su ka fi kudi a duniya

1. Real Madrid: 479.5m euros 2. Barcelona: 450.7m euros 3. Man Utd: 367m euros 4. Bayern Munich: 321.4m euros 5. Arsenal: 251.1m euros 6. Chelsea: 249.8m euros 7. AC Milan: 235.1.m euros 8. Internationale: 211.4m euros 9. Liverpool: 203.3m euros 10. Schalke: 202.4m euros

Bayanai: Deloitte: 2010-11