Kamata yayi a cire Capello tun a 2010

capello Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fabio Capello

Kamata yayi a cire Fabio Capello a matsayin kocin Ingila tun bayan kamalla gasar cin kofin duniya a 2010, in ji mai lura da hukumar kwallon Ingila Peter Coates.

Capello wanda ya jagoranci Ingila a gasar da aka buga a Afrika ta Kudu inda aka fitar da kasar a zagaye na biyu, ya ajiye aikinsa ne a ranar Laraba.

Coates ya shaidawa BBC cewar "Ingila ta taka mummunar rawa a gasar kofin duniya, kuma laifinsa ne bata je ko'ina ba".

Shugaban Stoke City din ya soki Capello akan cewar bai nuna sha'awar koyan harshen Ingilishi da kyau ba.

Tsohon kocin Real Madrid da AC Milan din ya koma Ingila ne a shekara ta 2008.

Dan kasar Italiyan ya jagoranci Ingila ta tsallake zuwa gasar cin kofin kwallon kasashen Turai da za a buga a Poland da Ukraine kafin ya ajiye aikinsa, amma kuma Coates na ganin cewar Capello bai taka rawar gani ba a matsayin kocin Ingila.

Karin bayani