CAF:Hayatou na son tazarce zuwa 2017

Issa Hayatou Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Caf Issa Hayatou

Shugaban hukumar dake kula da kwallon Afrika CAF, Issa Hayatou ya ce yanason ya kara mashi shekaru hudu akan mulki.

Taron masu ruwa da tsaki a harkar kwallon Afrika sun nuna goyon bayan cewar shugaba Issa Hayatou na bukatar karin wasu shekaru hudu akan mulki.

A watan daya gabata ne dan Kamarun ya bayyanawa kwamitin zartarwa aniyarsa ta neman karin wa'adi.

A taron da aka gudanar a ranar Juma'a a Libreville, mambobin Caf sun amince da bukatar Hayatou a zaben da za a gudanar a shekara mai zuwa.

Hayatou shine shugaban CAF tun a shekarar 1988.

Idan har aka sake zabensa a badi, zai cigaba da jan ragamar CAF har zuwa shekara ta 2017.

Karin bayani