Zan so in gaji Capello - In ji Redknapp

redknapp Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Harry Redknapp

Harry Redknapp ya ce zai karbi mukamin kocin Ingila idan aka bashi damar ya maye gurbin Fabio Capello.

Redknapp wanda a yanzu ke haskakawa tare da Tottenham Hotspur,ya ce " Akwai sauki akwai kuma wuya barin Spurs".

Da dama na ganin cewar dan Ingilan mai shekaru 64 shine zai maye gurbin Capello, wanda ya ajiye aikinsa bayan ana cire John Terry a matsayin kyaftin.

Hukumar dake kula da kwallon ta bayyana cewar watakila a dauki kocin riko don gasar cin kofin Turai a 2012 abinda kuma zai bada damar baiwa sabon koci hada aikin Ingila da kuma na kulob.