Man City na ci gaba da jan ragama a gasar Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Joleon Lescot yana zura kwallo

Joleon Lescott ne ya zura kwallo daya tilo da ya ba Manchester City a nasarar da ta yi a kan Aston Villa a gasar Premier ta Ingila.

Kafin wasan dai, City tana bayan Manchester United ne da maki daya.

Villa dai ta jajirce a wasan a yayinda City ta nemi ta karya lagonta, amma sai bayan sa'a dan ne Lescott ya samu zura kwallon da ya ba City nasara.

Mai tsaron gidan City, Joe Hart ya tare kwallon Darren Bent dab da a tashi wasan.

A yanzu haka dai City na gaban United ne da maki biyu.