Villas-Boas ya dau laifi bayan kashin da Chelsea ta sha

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Liverpool, Andre Villas Boas

Kocin Chelsea, Andre Villas-Boas ya bayyana kashin da kungiyarshi ta sha a hannu Everton da ci biyu da nema a matsayin rashin nasara mafi muni da kungiyar ta samu a bana.

Andre Villas Boas ya nace cewa laifinsa ne da kungiyar ta taka mumunar rawa a wasan.

Villas-Boas ya ce: "Wasan da muka buga shine mafi muni a kakar wasan bana, a gaskiya Everton ta taka rawar gani sosai.

"Zan koma in kara nazari, domin inganta wasanmu nan gaba."

A yanzu haka dai, Chelsea ta sako zuwa matsayin na biyar a teburin gasar Premier.