Zambia ta lashe gasar cin kofin Afrika

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan wasan Zambia na murnar zura kwallo

Zambia ta lashe gasar cin kofin Afrika a karo na farko bayan da ta doke Ivory Coast da ci takwas da bakwai a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Didier Drogba ya bararwa Ivory Coast fenarity a cikin lokaci, abun da kuma ya sa kasashen biyu sun tashi babu ci. A karin lokaci babu kasar da ta zura kwallo, abun da kuma yasa aka yi bugun daga kai sai mai tsaron gida.

A yayinda ake bugun fenarity dai, 'yan wasan kasashen biyu zun zura kwallaye bakwai kowannesu kafin dan wasan Ivory Coast Kolo Toure ya zubar da nashi kwallo, shima dai dan wasan Zambia Rainford Kalaba ya zubar da nashi nan take.

Gervinho ne dia kara bararwa Ivory Coast fenaritin na biyu.

Bayan ya barar ne kuma Stoppila Sunzu ya zura kwallon da ya ba Zambia nasara a wasan.