Eden Hazard ya ce zai koma Tottenham

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan Lille, Eden Hazard

Dan wasan Lille Eden Hazard ya shaidawa wani gidan talbijin a kasar Belguim cewa zai koma kungiyar Tottenham da ke Ingila a karshen kakar wasan bana.s summer.

Kungiyoyi da dama ne dai a Turai, da su ka hada da Real Madrid da Arsenal ke zawarcin dan wasan mai shekarun haihuwa 21.

"Ina ganin zan koma Tottenham. Babbar kungiya ce a Ingila," In ji Hazard.

"Zan koma Ingila, saboda akwai kwararrun 'yan wasa a kasar, ban sa hannu a kwantaragi ba, amma kwanannan zamu cimma yarjejeniya."

Hazard dai ya nuna cewa ya fi son ya koma Ingila a maimakon Spain.