Carlos Tevez zai dawo Man City a ranar Talata

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Carlos Tevez

Kungiyar Manchester City na ganin Carlos Tevez zai dawo kungiyar a ranar Talata domin ci gaba da horo.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 28, zai dawo filin horon kungiyar ne da ke Carrington, inda za'a gwada lafiyarsa a ranar Talata da safe.

Kocin Manchester City, Roberto Mancini ya ce zai yi maraba da dawowar dan wasan.

Tevez dai yaki ya tashi ya motsa jiki ne a wasan da kungiyar ta buga da Bayern Munich a watan Satumban bara.

Wannan ne kuma yasa kocin kungiyar, Roberto Mancini ya ce dan wasan ba zai kara taka masa leda ba/

"Ni da kungiyar bamu da matsalar dawowar shi." In ji Mancini.

Tevez ya yi asarar wajen fam miliyan 10 saboda rashin jituwar da ya samu da kungiyarsa.

An ci tararsa fam miliyan daya da dabu dari biyu saboda rashin da'ar da ya nuna bayan da yaki dawowa kungiyar horo.

Har wa yau kungiyar ta daina biyanshi albashin fam dubu dari biyu a kowanne mako.